in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu 'yan kunar bakin wake sun hallaka masallata 4 a Baman Najeriya
2018-04-23 10:54:33 cri

Wasu 'yan kunar bakin wake su biyu sun hallaka masallata 4, a wani masallaci dake garin Bama a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya.

Rahotanni sun tabbatar da jikkatar wasu karin mutanen 8 a harin na asubahin ranar Lahadi. Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, hakimin karamar hukumar ta Bama Buba-Shehu Gulumba, ya ce 'yan kunar bakin waken mace da namiji, sun kutsa kai cikin masallacin ne lokacin da ake tsaka da sallar asuba, suka kuma tada abubuwan fashewa dake jikin su. Ya ce, mutane 3 sun rasu nan take, yayin da dayan kuma ya rasu bayan an kai shi asibiti.

Rundunar 'yan sandan yankin ta ce, ta killace wurin da lamarin ya auku, tana kuma ci gaba da gudanar da bincike game da aukuwar lamarin.

Garin Bama dai na da nisan kilomita 67 a kudu maso gabashin birnin Maiduguri, fadar mulkin jihar ta Borno. Ya kuma sha fama da hare hare makamancin wannan, wadanda ake alakantawa da kungiyar Boko Haram mai da'awar jihadi. A karshen shekarar 2014, garin ya fada hannun kungiyar ta Boko Haram, kafin kuma a shekarar 2015 sojojin gwamnati su 'yanto shi.

MDD ta ce mayakan Boko Haram sun hallaka sama da mutane 20,000 tun daga shekarar 2009 kawo yanzu.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China