in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tabbatar da mutuwar mutane 25 a harin da aka kai a jihar Plateaun Najeriya
2018-03-14 09:25:39 cri

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 25 a wani harin da aka kaddamar kan al'ummar yankin Dundu, a jihar Plateau dake shiyyar tsakiyar Najeriyar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Plateau Terna Tyopev, ya shedawa 'yan jaridu cewa, maharan sun afkawa al'ummar yankin ne da yammacin ranar Litinin.

Tyopev ya ce, mutane biyu sun samu munanan raunuka, kana an cinnawa gidaje masu yawa wuta a lokacin da maharan suka kaddamar da farmakin.

Ya ce, tuni rundunar 'yan sandan ta kaddamar da shirin bincike domin bankado wadanda ake zargin kaddamar da harin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China