in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nijeriya zai koma London don duba lafiyarsa
2018-05-08 09:25:59 cri

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, zai yi tafiya zuwa birnin London a yau Talata, domin duba lafiyarsa.

Kakakin shugaban kasar Garba Shehu, ya ce a wannan karon, kwanaki 4 kawai shugaba Buhari zai yi a Birtaniya.

Ya ce, shugaba Buhari ya yi wata 'yar ganawa da likitansa a makon da ya gabata, lokacin da ya yada zango a birnin London, a kan hanyarsa ta komawa daga Washington bayan ziyarar da ya kai Amurka.

Garba Shehu ya ce, likitan ya bukaci shugaba Buhari ya koma, inda shugaban ya amince, yana mai cewa, shugaban zai koma gida Nijeriya ne a ranar Asabar.

A watan Junairun bara ma, shugaban ya je duba lafiyarsa a birnin na London, sai dai bai koma gida a lokacin da ya shirya komawar ba.

Bayan ya koma Abuja ne kuma ya tabbatar da cewa, ba shi da lafiya sosai, kuma bai taba shiga irin yanayin ba a rayuwarsa.

Ko a ranar 7 ga watan Mayun bara, wato shekara daya cif ke nan, ya kai irin wannan ziyara London, inda ya koma gida bayan ya shafe kwanaki 103. ( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China