in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan al'ummar Najeriya na karuwa da kaso 3.2 bisa dari a duk shekara
2018-04-27 12:40:38 cri

Shugaban hukumar kididdigar yawan al'umma ta tarayyar Najeriya Eze Duruiheoma, ya ce 'yan kasar na karuwa da kaso 3.2 bisa dari a duk shekara.

Eze Duruiheoma, ya shaidawa manema labarai hakan a Abuja, fadar mulkin kasar. Ya ce, bisa kiyasi yawan 'yan Najeriyar ya kai kusan mutane miliyan 198. Mr. Duruiheoma ya ce, akwai bukatar gudanar da kidayar jama'ar kasar domin tantance alkaluma na hakika. Ya ce, hakan zai tallafawa kasar gudanar da tsarin samar da ci gaba mafi dacewa.

A ranar 10 ga watan Afirilun nan ne dai mahukuntan kasar suka fidda wata sanarwa wadda ta bayyana cewa, yawan 'yan Najeriyar ya karu zuwa miliyan 198, yayin da yawan al'umma mazauna biranen kasar shi ma ke karuwa da kaso 6.5 bisa dari a duk shekara.

Sanarwar gwamnatin ta nuna cewa, mafiya yawa daga wadanda ke yin kaura zuwa birane daga yankunan karkarar kasar matasa ne, da mata, ciki hadda wadanda ke cikin shekarun su na haihuwa.

Wata kididdigar da aka yi a baya bayan nan ta nuna cewa, nan da shekara ta 2050, Najeriya za ta kai matsayi na 3 a jerin kasashe mafiya yawan al'umma a duniya. Yanzu haka dai ita ce kasa ta 7 a wannan jadawali.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China