in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasan opera na Beijing ya samu dandazon 'yan kallo a Najeriya
2016-11-22 10:22:49 cri

Daruruwan 'yan kallo a Abuja, helkwatar mulkin Najeriya ne suka kashe kwarkwatar idonsu a lokacin da suka kallon nune-nunen wasan opera na Beijing na kasar Sin wanda aka gudanar da yammacin ranar Lahadin da ta gabata.

Wasan na Sinawa mai kayatarwa, ya kunshi sanya tufafi masu kyawun launi don gudanar da raye raye da wakoki dake nuna al'adun Sinawa, kuma wannan kusan shi ne karon farko da wasan ya samu dinbin 'yan kallo a tarayyar Najeriya.

Wasan wanda cibiyar raya al'adun gargajiya ta kasar Sin dake Najeriya ta shirya, an shirya bikin ne domin murnar cika shekaru 45 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasar Sin da Najeriya.

Jakadan Sin a Najeriya Zhou Pingjian, ya bayyana cewa, wasan opera na Beijing wasan gargajiya mafi muhimmanci ne dake nuna al'adun kasar Sin. Kuma an shirya shi ne domin samar da dama ga al'ummar Najeriya da su kara fahimtar al'adun kasar Sin.

Jakada Zhou ya ce, dangantakar dake tsakanin Sin da Najeriya cikin shekaru 45 da suka gabata, ta haifar da gagarumin alfanu ga al'ummomin kasashen biyu, ya kara da cewa, za'a sake karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta hanyar musayar al'adu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China