in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan bindiga sun halaka mutane 11 a Najeriya
2017-11-09 10:22:56 cri

Rundunar 'yan sandan jihar Filato dake yankin tsakiyar Najeriya, ta sanar a jiya Laraba cewa, a kalla mutane 11 ne suka gamu da ajalinsu, kana wasu mutane 4 kuma suka ji rauni, lokacin da wasu 'yan bindiga suka bude wuta kan wasu kauyawa a kan hanyarsu ta dawo gida daga wata kasuwar kauye a yankin Riyom dake jihar ta Filato.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Terna Tyopev ya ce, lamarin ya faru ne a daren ranar Talata, sai dai har yanzu ba a kama kowa ba, amma jami'an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike don ganin an kamo maharan.

Wannan shi ne hari na baya-baya a jerin tashin hankalin dake faruwa a yankunan karkarar jihar, wadda musulumai suka fi rinjaye a bangaren arewaci, kana mabiya addinin kirista kuma ke da rinjaye a kudancin jihar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China