in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kara bude kofa a fannin hada-hadar kudi
2018-05-04 13:17:43 cri

Yayin dandalin tattalin arziki na Bo'ao da ya gudana a watan jiya, gwamnatin kasar Sin ta sanar da manufarta ta kara bude kofa a fannin hada-hadar kudi. Ya zuwa yanzu kasar ta dauki wasu takamaiman matakai a wannan fanni.

Matakan da gwamnatin kasar Sin ta sanar da dauka a yayin dandalin Bo'ao sun hada da soke tarnaki da aka sanya wa kamfanonin kasashen waje a fannin mallakar hannayen jarin banki ko kuma kamfanin sarrafa hannun jari da aka kafa cikin kasar Sin. Gami da kara yawan hannayen jarin kamfanonin hada-hadar kudi da kamfanonin kasashen waje za su iya mallaka zuwa kashi 51%, wani tarnakin da za a soke ta baki daya bayan wasu shekaru 3. Daga bisani, kamfanin "United Bank of Switzerland" ya fara neman kara mallakar hannayen jarin wani kamfanin da ya kafa a kasar Sin daga fiye da kashi 24% zuwa 51%.

Dangane da lamarin, mista Xie Yaxuan, kwararren mai nazarin harkokin hada-hadar kudi na kamfanin sarrafa hannayen jari na CMS, ya ce yadda aka fara aiwatar da matakan da aka sanar cikin sauri ya nuna sahihancin kasar Sin. A cewarsa,

"Ana gudanar da matakan cikin sauri, hakan ya nuna cewa, da farko, da gaske kasar Sin take wajen bude kofarta, da kara baiwa jarin waje damar shiga kasuwannin hada-hadar kudinta. Na biyu kuma, batun ya nuna yadda kamfanonin kasashen waje suke nuna sha'awa kan kasuwannin kasar Sin."

Haka zalika, Mista Xie ya ce, yadda aka kara bude kofar sana'ar harkokin hannayen jari a kasar Sin, wani mataki ne da zai biya bukatun wannan sana'a na raya kanta. Ya kara da cewa,

"Shigowar jarin waje za ta kara yanayin takara tsakanin kamfanoni daban daban a kasuwar hada-hadar kudi ta kasar Sin. Amma a sa'i daya, za ta sanya a samu karin kudin da za a zuba a kasuwar. Lamarin da zai taimakawa habakar kasuwar hada-hadar kudi, da bayar da karin damammaki ga wadanda ke kokarin neman riba a kasuwar."

Ban da haka, matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka wadanda suka shafi harkokin bankuna da kamfanonin inshora, su ma sun samu martani daga kamfanonin kasashen ketare. Ga misali, a ranar 2 ga watan Mayun da muke ciki, babban bankin al'ummar kasar Sin, kana babban baitulmalin kasar, ya sanar da cewa, wani kamfani mai jarin kasar Birtaniya da ake kira "World First" ya mika bukatar neman izinin gudanar da aikin biya da karbar kudi a kasuwannin kasar Sin. Wannan shi ne karo na farko da wani kamfanin ketare ya nemi iznin kula da sana'ar biyan kudi a kasar ta Sin.

Ban da haka, kamfanin Experian na kasar Birtaniya mai kula da aikin tantance sahihancin kamfani shi ma yana shirin kafa reshensa a cikin kasar Sin, wanda ya mika bukatar neman iznin samar da hidimar tantance sahihancin kamfani a cikin kasar Sin.

Dangane da wadannan batutuwa, Mista Zhao Xijun, mataimakin shugaban cibiyar nazarin harkokin kudi ta jami'ar Renmin ta kasar Sin, ya ce

"Ana iya cewa, yadda aka bude kofa a wannan karo, ya taba fannoni daban daban, kana matsayi na koli bisa tsarin tattalin arzikin kasarmu. Idan muka kalli matakan da aka dauka a shekarun baya, za a ga cewa su ma matakai ne na bude kofa. Sai dai a wannan karo, mun ga yadda aka baiwa kamfanonin kasashen waje tukwici iri daya da takwaransu na kasar Sin. Hakika yadda kasar Sin ta kara bude kofa shi ma ya samar da karin damammaki ga ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin kasa da kasa. Sa'an nan kamfanoni masu zuba jari, da masu gudanar da cinikayya, da masu kula da hada-hadar kudi, su ma sun samu karin damammaki bisa matakan da kasar Sin ta dauka."

A nasa bangare, kakakin kamfanin "United Bank of Switzerland" ya shaida gaskiyar maganar Mista Zhao, inda ya ce kasuwannin kasar Sin na da muhimmanci sosai ga bankin Switzerland, saboda haka yadda kasar Sin ta kara bude kofarta a fannin hada-hadar kudi wata babbar dama ce ga bankin domin ya kara habaka a kasuwannin kasar.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China