in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana farin ciki da martanin da Amurka ta mayar, sai dai matakai sun fi zance
2018-04-11 19:11:39 cri
A taron dandalin Boao na kasashen Asiya da aka bude jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi, inda ya bayyana matakan da kasarsa za ta dauka ta fannin kara yin gyare-gyare a gida, da kuma bude kofa ga kasashen waje, jawabin da ya samu yabo daga kasa da kasa, har ma shugaban kasar Amurka Donald Trump ya mai da martani na yin sassauci.

Kara bude kofa manufa ce da kasar Sin ke tsayawa tsayin daka a kai

A cikin shekaru 40 da suka wuce, kamar yadda shugaba Xi Jinping ya bayyana a jawabinsa, al'ummar kasar Sin sun tsaya tsayin daka a kan manufar bude kofa ga kasashen ketare, matakin da ya kasance wani babban sauyi ga kasar wadda a da ta rufe kofarta, har ma ya sa kasar take samar da tabbaci da kuzari ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya, kuma ta ba da gudummawa ga zaman lafiya da ci gaban dan Adam baki daya.

Sai dai Amurka za ta gamu da matsaloli idan ta nuna girman kai ko kuma kare kanta.

Shugaban babban bankin kasar Sin Yi Gang a yau Laraba ya sanar da hakikanan matakai, da ajandar habaka bude kofa ga kasashen waje a fannin hada hadar kudi. Wannan ya nuna cewa, ko da yaushe kasar Sin na cika alkawarin da ta yi. Ya ce idan Amurka ta tsaya ga tayar da yakin cinikayya, za ta rasa damar karfafa hadin kai tare da Sin, da kuma damar cin moriya sakamakon bude kofa ga kasashen waje da ci gaba na kasar ta Sin.

Ana maraba da Amurka da ta mai da martani na yin sassauci, amma sai dai matakai sun fi zance. Za a duba irin matakan da za ta dauka nan gaba. Ana kuma fatan Amurka ta gane yanayin da ake ciki.

A yanzu haka hadin gwiwar al'ummomin duniya baki daya shi ne ke dacewa da halin da ake ciki, wanda hakan ke bukatar tsarin cinikayya na tsakanin bangarori da dama, kana da yaki da ra'ayin warewa gefe daya, da bin manufar samun moriyar juna, ta yadda za a iya cimma nasara tare.(Lubabatu  Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China