in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF: kasar Sin za ta tabbatar da saurin bunkasar tattalin arzikinta
2018-04-18 13:38:06 cri

Asusun ba da lamuni na kasa da kasa wato IMF ya kaddamar da sabon rahotonsa, wanda ya yi hasashe kan tattalin arzikin kasa da kasa, inda a cewarsa, saurin bunkasar tattalin arzikin duniya ya kai kaso 3.8 cikin dari a shekarar 2017, wanda ya fi sauri a cikin shekaru 7 da suka wuce. Rahoton ya yi hasashen cewa, saurin ci gaban tattalin arzikin duniya a bana da kuma badi zai kai kashi 3.9 cikin dari, kamar yadda ya yi hasashe a watan Janairun bana. Sa'an nan saurin ci gaban tattalin arzikin kasar Sin a bana da kuma badi, zai kai kashi 6.6 cikin dari da kuma kashi 6.4 cikin dari. Amma rahoton ya yi gargadin cewa, akwai yiwuwar kafa shinge a harkokin ciniki da kuma matakan yaki da kafa shinge a harkokin cinikinsu sanyaya gwiwar mutane, ta yadda ba za a iya raya tattalin arzikin duniya yadda ya kamata ba.

"Ga alama tattalin arzikin duniya yana ci gaba da bunkasa a fannoni daban daban, amma duk da haka, takaddamar cinikayya a tsakanin wasu bangarori ta samar da rashin jituwa a duniya."

Maurice Obstfeld, babban masanin ilmin tattalin arziki na asusun IMF shi ne ya bayyana haka a yayin taron kaddamar da rahoton IMF da ya yi hasashe kan tattalin arzikin kasa da kasa a jiya, inda ya kuma nuna amincewa kan alamar ci gaban tattalin arzikin kasa da kasa a halin yanzu da kuma nan gaba ba da dadewa ba. Amma duk da haka, mista Obstfeld ya ambato rashin jituwa a cikin jawabinsa, wato takkaddamar cinikayya da ke tsakanin manyan rukunonin tattalin arziki a duniya a kwanankin baya. "Takkardamar ciniki da ke tsananta a kwanakin baya ta fara ne daga matakin da kasar Amurka ta sanar na kara kudin haraji kan kayayyakin karfe da samholo sakamakon dalilin tsaron kasa a farkon watan Maris na bana. Lamarin ya sanya Amurka da kasashe abokan cinikinta yin shawarwari, domin rage gibin ciniki dake tsakaninsu. Amma abu ne mai wuya, wadannan matakai su rage gibin ciniki da Amurka take fuskanta. Babban dalilin da ya haifar da irin wannan gibin ciniki shi ne, yawan kudaden da kasar ta Amurka ta kashe sun fi kudaden da ta samu. Hakika dai matakan hada-hadar kudi da Amurka ta dauka a kwanan baya sun kara gibin ciniki da take fuskanta."

Asusun na IMF ya kuma yi hasashen cewa, a shekarar 2019 mai zuwa, gibin ciniki da kasar Amurka za ta fuskanta zai kai misalin dala biliyan dari 1 da 50. Amma mista Obstfeld ya bayyana cewa, ko da yake ana fuskantar takkaddamar ciniki mai zafi, yana ganin cewa, ya zuwa yanzu kasashen duniya za su iya magance barkewar yakin ciniki ta hanyar yin shawarwari a tsakanin bangarori daban daban. "Ko da yake wasu sun yi kashedi kan takkardamar ciniki, amma ga alama takkardamar ciniki ne, ba yakin ciniki ba. A ganina, ya zuwa yanzu, kasashen duniya za su iya kara tattaunawa a tsakanin bangarori daban daban, a kokarin magance tsanantar takkardama ta hanyar da ake bi a yanzu wajen daidaita takkardamar."

Kowa na sane da amfanin ciniki a fannonin bunkasar tattalin arzikin kasa da kasa da kuma yaki da kangin talauci. Mista Obstfeld ya jaddada cewa, babu wanda zai ci nasara cikin yakin ciniki. Ba za a iya kara azama kan kara bude kofa a harkokin cinikayya ba, sai dai an daidaita sabani bisa tsarin bangarori daban daban. "Yaya za a kau da rashin adalci a harkokin ciniki, ciki har da batun kiyaye ikon mallakar fasaha? Wajibi ne a daidaita sabani cikin adalci yadda ya kamata bisa tsarin bangarori daban daban. Ya kamata a inganta tsare-tsaren da ake amfani da su a yanzu, a maimakon yin barazana ga cinikayya tsakanin bangarori biyu."

Har ila yau, sabon rahoton asusun na IMF, ya sake bayyana cewa, kasashen duniya za su kara dogaro da juna a nan gaba. Kuma yin hadin gwiwa a tsakanin bangarori daban daban, hanya ce mai dorewa da za a iya bi wajen daidaita mabambantan kalubale a fannonin tafiyar da harkokin cinikayyar kasa da kasa, sauyin yanayi, yaduwar cututtuka, tsaron kai a yanar gizo ta Intanet, dora kudin haraji kan kamfani da dai sauransu. In ba haka ba, tattalin arzikin kasa da kasa ba zai bunkasa ba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China