in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Red Cross da IFRC sun alkawarta fadada tallafi ga masu gudun hijirar Falasdinu da Syria
2018-02-05 13:52:13 cri

Kungiyar ba da tallafin jin kai ta Red Cross da takwararta ta Red Crescent Societies ko IFRC, sun alkawarta ci gaba da tallafawa fararen hula dake cikin matsananciyar bukatar agajin jin kai, kamar dai yadda mataimakin shugaban IFRC Chen Zhu ya bayyana.

Mr. Chen ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai sansanin 'yan gudun hijira na Guob Elias dake gabashin kasar Lebanon, tare da rakiyar jakadan Sin a Lebanon Wang Kejian.

Jami'in na IFRC ya samu tarba daga jami'an Red Cross, wadanda kuma suka bayyana masa halin da ake ciki a sansanin, da yanayin mazauna sansanin, tare da bukatun lafiya da na ilimin su.

Mr. Chen, wanda ke rike da mukamin jagoran Red Cross Society na Sin, ya ce kungiyar reshen kasar Sin na fatan yin hadin gwiwa da takwararta ta Falasdinu, wajen inganta rayuwar 'yan gudun hijira dake sassa daban daban na duniya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China