in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An ce kafa kasashe biyu ginshikin zaman lafiya ne tsakanin Isra'ila da Palestinu
2017-03-30 10:50:17 cri

MDD, da kungiyar tarayyar Turai, da shugabannin kungiyar kasashen Larabawa sun tabbatar a jiya Laraba cewa, babu wata mafita muddin a ba bukatar samar da dawwamaman zaman lafiya ta hanyar kafa kasashe biyu a Palastinu da Isra'ila wadanda ke yin gaba da juna a cikin shekaru goma da suka gabata.

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya fada a lokacin taron kasashen Larabawa karo na 28 a Jordan cewa, warware rikicin dake tsakanin Palestinu da Isra'ila ta hanyar kafa kasashe biyu zai samar da zaman lafiya mai dorewa, da tsaro, da mutunta dan adam ga al'ummomin sassan biyu.

Guterres ya ce, babu wani mataki na biyu baya ga wannan, idan dai ana maganar tabbatar da zaman lafiya ne tsakanin bangarorin biyu. Ya ce, shi ya sa ya zama dole a yi watsi da duk wata manufa ta goyon bayan wani bangare daya.

Babban jami'in MDD ya kara da cewa, dole ne a dakatar da batun mamayar matsugunai ba bisa ka'ida ba, wanda kuma yin hakan ya saba da dokokin kasa da ksa.

Federica Mogherini, babban wakilin kungiyar EU mai kula da hulda da kasashen duniya da tabbatar da tsaro ya ce, kafa kasashe biyu dabara mafi dacewa ce yayin da ake warware matsalar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China