in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mozambique ta samu gagarumin ci gaba wajen kare namun daji
2018-05-03 10:26:04 cri

Mamba a sakatariyar CITES, wato yarjejeniya tsakanin kasa da kasa mai tabbatar da kare tsirrai da namun daji, Ben Van Rensburg, ya ce kasar Mozambique ta samu gagarumar nasara a fannin alkinta na kare namun daji ta hanyar magance laifukan dake barazana gare su.

Van Rensburg ya bayyana haka ne a jiya, yayin taron CITES da ya samu halartar wakilai 25 daga kasashen da suka cimma yarjejeniyar, domin tattauna manufofin da hadin gwiwa kan kawo karshen cinikayyar hauren giwa ba bisa ka'ida ba.

Ya ce, yadda ake kawar da laifukan dake barazana ga namun daji kamar samar da wajen adana namun daji na Gorongosa dake tsakiyar Mozambique, nasara ce mai muhimmanci da karfafa gwiwa.

Ya ce, wannan yunkuri da sauran ire-iren su ne dalilin da ya sa yawan giwaye ke karuwa a gidan adana namun daji na Gorongosa.

A nata bangaren, jakadiyar Birtaniya a Mozambique Joana Kuenssberg, cewa ta yi, kamata ya yi a sauya yadda ake zaburar da masu aikata laifukan da ke barazana ga namun daji.

Ta ce, suna son samun dorewar hadin gwiwa cikin lokaci mai tsawo, tare da karfafawa masu cinikayyar dabbobi gwiwar watsi da harkokinsu, tana mai cewa, kare safarar dabbobi ba bisa ka'ida ba a wuri irin Mozambique, hakki ne na duniya baki daya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China