in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwammnatin Mozambique ta karyata zargin MDD na sayan makamai daga DPRK
2017-09-28 09:52:21 cri

Ministan tsoron kasar Mozambique Atanasio M'tumuke ya karyata zargin da MDD ke yiwa kasarsa game da sayan makamai da na'urorin soja daga wani kamfanin kasar Koriya ta arewa wato DPRK.

Shi ma ministan harkokin kasashen waje da hadin gwiwa na kasar ta Mozambique Oldemiro Baloi ya yi watsi da zargin da MDD ke yiwa kasar tasa game da wannan batu, amma ya amince cewa, kasarsa ta dade tana alaka da Koriya ta arewa.

Rahotanni na cewa, kasar Mozambique tana daga cikin kasashen Afirka 11 wadanda suka keta takunkumin hana sayen makamai da MDD ta kakabawa Koriya ta arewa. Sauran kasashen sun hada da Angola, Jamhuriyar demokiradiyar Congo, Eritrea da Namibia, da Tanzaniya, da Uganda da Benin, da Botswana, da Mali da kuma kasar Zimbabwe.

Makonni biyu da suka gabata ne dai, kwararru a kwamitin sulhun MDD suka bayyana a cikin wani rahoto cewa, wani kamfanin zuba jari karkashin ma'aikatar tsaron kasar Mozambique, ya biya Koriya ta arewa dala miliyan 6 na makaman da kasar ta saya, hakan ya keta takunkumin hana sayar da makaman da MDD ke kakabawa Koriya ta arewan, zargin da bangaren Mozambique din ya karyata. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China