in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Renamo a Mozambique za ta tsakaita bude wuta na mako guda
2016-12-28 13:10:15 cri

Babbar jam'iyyar 'yan adawa ta kasar Mozambique Renamo ta sanar a jiya Talata cewa, dakarunta za su tsakaita bude wuta har na tsawon kwanaki 7.

Sanarwar ta Renamo ta zo ne kwana guda bayan babban madugunta Afonso Dhlakama ya yi wata zantawa ta wayar tarho da shugaban kasar Mozambique Filipe Nyusi, wanda ya kai ziyarar aiki a arewacin lardin Nampula, wanda shi ne lardi mafi yawan jama'a a kasar.

Madugun 'yan adawar ya bayyana cewa, jam'iyyar adawar ta dauki wannan mataki ne domin baiwa alummar kasar ta Mozambican damar gudanar da shagulgulan shekara cikin kwanciyar hankali.

Dama dai tun a ranar Litinin, shugaba Nyusi na kasar yake fatar jam'iyyar adawar ta dauki wannan mataki, bayan wata tattaunawa mai armashi da ta gudana tsakanin bangarorin biyu ta wayar tarho.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China