in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana gaf da kammala aikin ginin gada mafi tsawo a Afrika
2018-03-13 10:47:15 cri

Kamfanin gina tituna da gadoji na kasar Sin ya kammala kashi 95 bisa 100 na aikin ginin doguwar gadar nan da ta hada Maputo Bay, a kasar Mozambique, inda za ta hade babban birnin kasar Maputo da garin Catembe, kamar yadda Maputo Sul, kamfanin dake gudanar da aikin na Mozambique ya sanar.

Manajan dake duba ingancin aikin na Maputo Sul, Basilio Dzunga, ya bayyana cewa, idan aka kammala sake tsugunar da mutanen dake yankunan da aikin ginin gadar zai shafa, ana sa ran aikin zai kammala zuwa watan Yunin wannan shekarar.

Idan aikin ginin gadar ya kammala, rayuwar dubban mutanen dake rayuwa a bangarorin gadar ba za su fuskanci wata matsalar rashin kananan jiragen ruwan fito ba, wanda shi ne babbar hanyar da ake amfani da ita wajen sada al'ummomin dake bangarorin biyu, wanda a mafi yawan lokuta ake samun ko rashin ingancin jiragen ruwan fiton, ko kuma lalacewar jiragen ruwan da ake fito da su.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China