in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da na'urar bada magani ta farko a kasar Afrika ta kudu
2018-03-16 09:54:47 cri
Sashen kiwon lafiya na lardin Gauteng na kasar Afrika ta kudu tare da hadin gwiwar kungiyoyin kiwon lafiya samar da magunguna na "Right to care da Right epharmacy", sun kaddamar da wata gagarumar na'ura ta bada magani mai kama da naurar ATM da ake wa lakabi da ATM Pharmacy ko PDU.

Na'urar ta PDU, ita ce irinta ta farko a nahiyar Afrika da ayarin kwararru daga Jamus suka samar, wadda kuma ake sa ran za ta sauya tsarin kiwon lafiya a kasar.

Na'urar za ta rika samarwa masu cututtuka masu tsanani da suka hada da Kanjamau da ciwon suga da tarin fuka magungunansu bayan mintuna 3-3.

Na'urar mai kama da ATM na amfani ne da lantarki da kuma fasahar intanet domin ganowa tare da zaba da bada maganin da aka rubutawa marasa lafiya.

A cewar Gwen Ramokgopa dan majalisar zartawa mai kula da kiwon lafiya a Gauteng, ana sa ran PDU din za ta taimaka wajen rage cunkoson jama'a a asibitoci. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China