in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu 'yan daba sun kutsa zauren majalisar dattijan Najeriya suka dauke sandar majalisar
2018-04-19 09:49:05 cri

Wasu 'yan bangar siyasa sun kutsa zauren majalisar dattijan Najeriya a jiya Laraba, inda suka yi awon gaba da sandar majalisar a lokacin da majalisar ke zamanta.

Yan dabar sun yi galaba a kan jami'an tsaro, sun tsere cikin wata motar dake jiran su a wajen harabar ginin majalisar dattijan kasar, inda suka gudu da sandar majalisar.

Majalisar dattijan kasar ta yi Allah wadai da faruwar lamarin, inda ta bayyana shi da cewa tamkar cin zarafi ne ga tsarin demokaradiyya.

Ana zargin wani sanata wanda majalisar ta dakatar da shi daga aiki a makon jiya da laifin daukar nauyin sace sandar majalisar, kakakin majalisar dattijan ne ya tabbatar da hakan.

Sanata Ovie Omo-Agege, wanda ke wakiltar jihar Delta mai arzikin mai, a makon jiya ne majalsiar dattijan ta dakatar da shi daga bakin aiki na tsawon kwanaki 90, bayan da ta zarge shi da laifin kin amincewa da dokar sauya lokutan zaben kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China