Kafar yada labaran Isra'ila ta ce an kai harin ne sansanin kungiyar Hamas dake gabas da sansanin 'yan gudun hijira na al-Mughazi dake tsakiyar zirin Gaza, a wani mataki na mayar da martani ga rokokin da aka harba daga Gaza zuwa yankin kudancin Isra'ila.
Majiyoyi daga jami'an tsaron Falasdinu na cewa, motocin yakin Isra'ila 2 sun harba ababen fashewa zuwa sansanin soji dake tsakiyar Zirin Gaza, inda suka ce babu wanda ya ji rauni, sai dai harin ya yi barna sosai ga sansanin dake kusa da iyaka da Isra'ila.
Wani shaidar gani da ido ya ce, a jiya Alhamis, an harba makaman roka daga zirin Gaza zuwa kudancin Isra'ila domin mai da martani ga matakin Amurka na ayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila.
Kawo yanzu dai, babu wanda ya dauki alhakin harba makaman rokar.(Fa'iza Msutapha)