in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron 'yan majalissar kungiyar ECOWAS
2018-04-25 11:28:28 cri
An bude taron 'yan majalissar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS a jiya Talata a binrin Banjul na kasar Gambia, inda ake sa ran cikin kwanaki 5, mahalarta taron za su tattauna game da batutuwa masu nasaba da sauyin yanayi, da kuma harkokin inganta noma a shiyyar.

Kakakin majalissar Mustapha Ceesay Lowe, ya ce taron zai nazarci yunkurin da ake yi na hade sassan yankin wuri guda. Ya ce matsalolin inganta noma, da na kare aukuwar kamfar abinci, na ci gaba da zama kadangaren bakin tulo ga shiyyar, duk kuwa da irin tsare tsare, da matakai daban daban da ake dauka don kawo karshen hakan.

A nata tsokaci, kakakin majalissar dokokin kasar Gambia Mariam Jack Denton, ta ce matakan da ya dace a lura da su sun wuce batun fidda tsare tsare kadai, duba da cewa akwai kalubale na karancin ruwan sama, da kuma tasirin sauyin yanayi. Mariam ta ce dole a yi la'akari da dukkanin wadannan kalubale, a kuma zakulo hanyoyin warware su yayin wannan taro.

Ta kara da cewa, bunkasa samar da amfanin gona da ci gaban nahiyar Afirka na fuskantar babbar barazana daga karancin ruwan sama a wasu sassan nahiyar. Don haka a ganin ta, akwai bukatar duba sabbin dabarun da za su ba da damar kyautata yanayi, da zuba jari a fannin, da shigar da sakamakon kirkire kirkire, wadanda za su taimaka wajen warware matsalolin da ake fuskanta.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China