in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ECOWAS ta sanar da sanya wa Guinea Bissau takunkumi
2018-02-02 13:25:31 cri

Tawagar manyan jami'an kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ta sanar da cewa, daga jiya Alhamis, kungiyar ta fara aiwatar da takunkumi kan 'yan siyasa da kungiyoyin siyasar Guinea Bissau a hukumance, saboda Guinea Bissau din ta ki martaba yarjejeniyar birnin Conakry.

Tawagar ECOWAS din karkashin shugabancin ministan harkokin waje da hadin gwiwa na kasar Togo mista Robert Dussey ta sanar da hakan ne a birnin Bissau, fadar mulkin kasar ta Guinea Bissau.

Mr. Dussey ya karanta sanarwar a filin jirgin sama na Bissau, inda ya kara da cewa, Guinea Bissau ba ta nada firaministan kasa wanda sassa daban daban suka amince da shi ba kamar yadda yarjejeniyar Conakry ta bukata. Kuma ba ta kafa gwamnatin kasa wadda ta bude kofa ga sassa daban daban ba, kana ba ta biya bukatun gudanar da zaben 'yan majalisa, wanda zai bude kofa ga sassa daban daban. Sai dai kuma Dussey bai fayyace tanade-tanaden da ke kunshe cikin takunkumin ba.

Har ila yau ECOWAS ta yi kira ga kungiyar tarayyar Afirka wato AU, da kungiyar hadin kan kasashe masu magana da harshen Portugal, da kungiyar tarayyar Turai wato EU, da MDD cikin gaggawa su ma su sanya wa Guinea Bissau takunkumi. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China