in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya ba da umurni kan mummunan hadarin mota da ya rutsa da Sinawa masu yawon shakatawa a Koriya ta Arewa
2018-04-23 20:30:42 cri

Jiya Lahadi da misalin karfe 6 na yamma, aka yi wani mummuman hadarin mota a yankin arewacin Hwanghae a kasar Koriya ta Arewa, inda babbar motar fasinja dauke da Sinawa masu yawon shakatawa 34 ta fado daga wata babbar gada.

Ya zuwa yanzu, Sinawa masu yawon shakatawa 32 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 2 kuma suka ji mummunan rauni.

Bayan abkuwar hadarin, kwamitin tsakiya na JKS da majalisar gudanarwar kasar Sin sun mai da hankali sosai kan hadarin. Shugaba Xi Jinping na kasar ya ba da umurni nan take, inda ya bukaci ma'aikatar harkokin wajen kasar da ofishin jakadancin kasar Sin da ke Koriya ta Arewa su dauki dukkan matakan da suka wajaba, na ganin an taimaka wa hukumomin Koriya ta Arewa da abin ya shafa wajen daidaita duk wasu abubuwan da suka shafi hadarin. Sa'an nan shugaba Xi ya bukaci a taimakawa wadanda suka ji rauni, da wadanda hadarin ya rutsa da su. Wajibi ne hukumomin wuraren da masu yawon shakatawa suka fito su yi kokarin kwantar da hankalun iyalinsu yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China