in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: Hare haren da ababen fashewa sun hallaka mutane 16 a Borno
2017-06-27 09:36:13 cri

Kwamishinan 'yan sandan jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya Damian Chukwu, ya ce a kalla mutane 16 sun rasa rayukan su, kana wasu 13 sun ji raunuka, yayin wasu hare haren da ababen fashewa da aka kaddamar a daren ranar Lahadi, a sassan jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Mr. Chukwu ya ce, 'yan sanda masu aikin kwance bama-bamai, sun isa wuraren da aka samu fashewar, yayin da aka gaggauta kai wadanda suka jikkata zuwa asibitoci.

Wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jihar ya rawaito cewa, wasu 'yan kunar bakin wake ne suka tsara kaddamar da hare hare a jami'ar gwamnatin tarayya dake birnin Maiduguri, da kuma unguwar Zannari dake birnin Maiduguri, fadar mulkin jihar.

Ya ce, an fara jin karar ababen fashewar tun da misalin karfe 10 na daren ranar ta Lahadi daga wasu sassan na jami'ar Maiduguri, wanda hakan ya tada hankulan da dama daga al'ummun dake cikin ta.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China