in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba za a gamu da matsalar sha'anin kudin da Sin ba za ta iya warware ba, in ji gwamnan babban bankin kasar Sin
2018-04-22 17:17:59 cri
Gwamnan bankin al'umma na kasar Sin Yi Gang,wato babban bankin kasar, ya bayyana jiya a Washington.D.C, babban birnin Amurka cewa, tushen tattalin arzikin kasar Sin ya na da karfi sosai, shi ya sa, ba za a iya haifar da matsalar kudi da kasar ba za ta iya warwarewa ba. A sa'i daya kuma, kasar Sin za ta iya daukar matakai da dama na tunkarar kalubalen da ya shafi harkokin kudi.

A jiyan ne aka kammala taron ministoci karo na 37 da hukumar gudanarwar Asusun ba da lamuni na IMF ya kira, inda Yi Gang ya sanar da cewa, a halin yanzu, bunkasar tattalin arzikin kasar Sin na da karfi sosai, kuma kasar tana da isassun manufofin fuskantar kalubalen da mai yiyuwa za ta gamu da su. Haka kuma, ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da habaka ayyukan gyara tsarin sha'anin kudi bisa ka'idar bude kofa ga waje, domin janyo hankulan masu zuba jari na kasa da kasa da kuma dukufa wajen habaka aikin shigowar hajoji daga ketare. Ban da haka kuma, za ta karfafa ayyukan kare ikon mallakar fasaha a duk fadin kasar.

Da yake tsokaci kan takaddamar ciniki dake tsakanin Sin da Amurka, Mr. Yi ya ce, ya kamata bangarori daban daban da abin ya shafa su ci gaba da habaka hadin gwiwar dake tsakaninsu, domin kiyaye tsarin ciniki tsakanin kasa da kasa a duniya yadda ya kamata. Kana, ya dace a yi amfani da tsarin wajen warware takaddamar ciniki dake tsakanin Sin da Amurka, yayin da ake kokarin inganta dunkulewar ayyukan zuba jari da cinikayya tsakanin kasa da kasa. Ya kara da cewa, ya kamata kasa da kasa su ci gaba da yin hadin gwiwa domin gaggauta gyara tsarin sha'anin kudi, ta yadda za a kara karfin bangaren a duniya.

Gwamnan babban bankin kasar Sin, ya jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga tsarin ciniki tsakanin kasa da kasa, yayin da take karfafa hadin gwiwarta da sassa daban daban.

A ko wace shekara, hukumar gudanarwar kan kira taro sau biyu, domin tattaunawa kan yanayin tattalin arzikin duniya da kuma ba da shawara ga ayyukan Asusun ba da lamuni na IMF. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China