in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanin Amurka: Cigaba da tattaunawa ne kadai hanyar magance takaddama tsakanin Sin da Amurka
2018-04-15 17:19:21 cri

Wani fitaccen masanin kasar Amurka ya bayyana cewa, jajurcewa wajen cigaba da tattaunawa ita ce kadai hanya mafi dacewa da za ta sassauta sabanin dake tsakanin kasashen Sin da Amurka, wadanda su ne kasashe biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya.

A jawabin da ya gabatar a yayin bude taron koli kan kasar Sin na Wharton na 2018, masani Geoffrey Garrett, shugaban tsangayar Wharton a jami'ar Pennsylvania, ya ce, kasar Sin ba wai kawai ta kasance kasa mafi karfin tattalin arziki a duniya ba ne, har ma ta kasance a matsayin jigo ta ko wace fuska ga harkokin duniya baki daya, kana kasar za ta cigaba da taka muhimmiyar rawa a harkokin duniya a karni na 21.

Ya ce, "Tabbas gaskiya ne akwai sabanin ra'ayi a tsakanin Sin da Amurka, amma idan ka dauki batun kasuwanci da tattalin arziki, za ka ga cewa akwai abubuwa masu ban sha'awa, saboda sabani yana iya bada damar taimakekeniya, da cimma matsaya tsakanin juna, da kuma bada damar yin hadin gwiwa don cin moriya tare."

Garrett ya ce, bunkasuwar da kasar Sin ta samu cikin sauri ya taimakawa cigaban tattalin arzikin Amurka a shekaru masu yawa.

Ya kara da cewa, alal misali, kamfanin kera motoci na General Motors, wanda shi ne kamfani mafi muhimmanci a tarihin Amurka, ba don abokan huldarsa na kasar Sin da kuma kasuwannin kasar Sin ba, da ya durkushe da kuma gaza cigaba da gudanar da aikinsa a lokacin da aka gamu da rikicin tattalin arziki a shekarar 2008.

A watan Afrilun shekarar 2016 ne aka kaddamar da kira taron kolin shekara shekara kan kasar Sin na Wharton, kuma ya kasance taron kolin dalibai mafi girma da ake gudanarwa game da kasar Sin a Amurka. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China