in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zargin Amurka kan Sin game da yayata fasaha da kuma ikon mallakar ilmi ba shi da kan gado
2018-04-09 10:45:19 cri

Sakamakon yawan tsokanar da kasar Amurka take yi a sau da dama ne ya haifar da takkadamar ciniki a tsakanin kasashen Sin da Amurka ta kara tsananta a 'yan kwanakin baya. Amurka ta bata wa kasar Sin suna bisa sakamakon bincike mai lamba 301, inda ta zargi gwamnatin Sin da tilastawa wasu kamfanonin kasar Amurka yayata fasahohinsu, wasu masana ilmin kudi da tattalin arziki sun bayyanawa manema labaru cewa, zargin da Amurka ta yi ba shi da kwararan shaidu. Kamfanonin Sin da Amurka suna yayata fasaha a tsakaninsu ne don radin kansu, kamfanonin Amurka sun samu riba mai yawa yayin da suke hada kai da takwarorinsu na Sin.

Li Wei, shugaban sashen nazarin nahiyoyin Amurka da Oceania na cibiyar nazari karkashin shugabancin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya yi nazari kan ainihin manufar Amurka na daukar wannan mataki, wato hakika dai Amurka na yunkura matsawa Sin lamba ne kan manyan manufofin tattalin arzikinta, kana tana kuma damuwa ganin cewa kasar Sin ta fita karfi a fannin fasaha.

Har ila yau kuma, Cui Fan, shehun malami a kwalejin nazarin ciniki da tattalin arzikin kasa da kasa a jami'ar ilmin cinikin waje da tattalin arzikin waje ta kasar Sin yana ganin cewa, manufar Amurka na daukar wannan matakin shi ne, tana son nunawa kasar Sin bambanci wajen kara haraji kan kayayyakin da Sin take sayarwa a Amurka, ana iya cewa, ta yayyaga takardar sunayen fannoni da ta yi alkawarin yin rangwame da rage kudin haraji a karkashin kungiyar ciniki ta kasa da kasa wato WTO. Matakin nata ya sabawa ka'ida mafi muhimmanci ta kungiyar ta WTO kai tsaye. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China