A sakon da ya aike masa jiya Alhamis, Shugaba Xi ya ce kasashen Sin da Cuba 'yan uwa ne kuma abokai, kana abokan hulda da suka aminta da juna, wadanda ke da makoma iri guda, yana mai cewa kasashen biyu sun kulla aminci ne ta hanyar doguwar gwagwarmaya mai wahala da su sha, wadda ta zama muhimmiya wajen inganta ci gaba da dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Shugaba Xi ya ce a halin da ake ciki yanzu, inda ake fuskantar sauye-sauye masu sarkakiya a yankuna da ma duniya baki daya, Sin da Cuba sun shiga wani sabon babi na cimma nasara, ya na mai cewa a shirye Sin take, ta hada hannu da Cuba kan abubuwan da za su kai su ga samun ci gaba.
Ya kara da cewa, a shirye yake ya yi aiki da Diaz-Canal wajen kara zurfafawa tare da fadada alakar dake tsakanin kasashensu, da kuma samun sabbin nasarorin da za su daukaka abotar da ke tsakaninsu a wannan sabon zamani. (Fa'iza Mustapha)