in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da manzon musamman na shugaban Cuba
2016-06-27 20:09:38 cri
A yau ne a nan birnin Beijing shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da Salvador Valdes Mesa manzon musamman na shugaban kasar Cuba Raul Castro.

A jawabinsa shugaba Xi ya ce, ya yaba da irin nasarorin da kasar Cuba ta samu a cikin sama da shekaru 50 da suka gabata.

Ya kara da cewa, ya yi imanin al'ummar kasar Cuba za su kara samun nasarori a nan gaba karkashin jagorancin sabon kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Cuba (PCC) wadda Raul Castro ke zama babban sakatarenta.

Xi ya ce, dangantaka tsaanin Sin da Cuba ta jure canje-canjen da duniya ke fuskanta, kana kasashen biyu suna da ra'ayi daya kana suna la'akari da abubuwan da ke damun juna.

A nasa jawabin Valdes ya ce, bangaren Cuba ya yaba da dadadden zumuncin da ke tsakanin Cuba da Sin, kuma sabbin shugabannin kasar suna dora muhimmanci kan dangantakar da ke tsakanin jam'iyyun siyasu da kuma kasashen biyu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China