in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta tura jami'an kiyayen zaman lafiya 395 zuwa Mali
2018-04-19 11:15:11 cri

Kasar Sin za ta tura dakarun kiyaye zaman lafiya na shirin MDD kimanin 395 zuwa kasar Mali a watan Mayu don gudanar da aikin samar da zaman lafiyar na tsawon shekara guda.

A ranar Laraba ne aka kaddamar da shirin tura jami'an a hukumance, wannan ita ce bataliya ta 6 na jami'an wanzar da zaman lafiyar da kasar Sin ta tura zuwa Mali.

Jami'an sun hada da dakarun tsaro 170, da dakarun tsaron masamman su 155 da kuma jami'an kiwon lafiya 70.

Jami'an za su gudanar da ayyukan da suka hada da gyara titunan mota, da gadoji da kananan hanyoyi a yankunan da ake aikin wanzar da zaman lafiyar, da aikin tabbatar da tsaron helkwatar shirin wanzar da zaman lafiyar, da kuma kula da marasa lafiya da duba lafiyar wadanda suka samu raunuka.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China