A jiya Talata ne kwamitin sulhun MDD ya zartas da wani kuduri mai lambar 2374, inda aka tsai da kudurin cewa, za a sanya takunkumi ga mutane ko kamfanoni dake daukar matakan gurgunta yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar Mali.
Takunkumin dai zai iya zama na hana tafiye-tafiye, da kuma hana amfani da kadarorinsu, kana domin aiwatar da takunkumin, za a kafa wata hukuma ta musamman.
A dai wannan, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya fitar da wata sanarwa, inda ya yi suka ga harin da aka kaiwa ayarin motocin rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya dake Mali a jiya Talata, harin da ya haddasa rasuwar sojojin kiyaye zaman lafiya guda biyu, tare kuma da jakkata wasu saura guda biyu.(Jamila)