in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aljeriya tana da muhimmanci wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar Mali, in ji firaministan Mali
2018-01-15 08:46:31 cri

A jiya Lahadi ne, firaminisan kasar Mali Soumeylou Boubeye Maiga ya kammala ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya kai kasar Aljeriya, kasar da Maiga ya bayyana a matsayin mai muhimmancin gaske wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar kasar da aka cimma.

Bugu da kari, yayin wannan ziyara, Maiga ya tattauna batun tsaro a yankin Sahel da mahukuntan kasar ta Aljeriya, yana mai cewa, kasashen biyu sun amince su karfafa alaka a wannan fanni. Kuma nan ba da dadewa ba wata tawaga daga kasar ta Mali za ta ziyarci Aljeriyar don ganin an cimma wannan buri.

Ko da a ranar Asabar din da ta gabata ma sai da Maiga ya gana da takwaransa na kasar Aljeriya Ahmed Ouyahia, inda ya bukaci kungoiyoyin 'yan aware dake arewacin kasar Mali da su hada kai da gwamnatin Mali don ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a makwabciyar kasar.

Ouyahia ya kuma shaidawa taron manema labarai da suka shirya tare da takwaransa na Mali cewa, kasarsa na karfafawa kungiyoyin 'yan tawayen Mali gwiwar daukar kwararan matakan sasantawa da mahukuntan Mali don ganin zaman lafiya ya tabbata a kasar.

A shekarar 2015 ne dai kasar Aljeriya ta taka rawa a yarjejeniyar zaman lafiya da sasantawa da aka sanyawa hannu, a wani mataki na kawo karshen tashin hankalin dake faruwa tsakanin gwamnati da 'yan aware da kuma kungiyoyi masu dauke da makamai dake arewacin Mali. Yarjejeriyar da dukkan sassa da ba sa ga maciji da juna a Mali suka amince da ita, bayan tattaunawa har sau biyar da MDD ta jagoranta a watan Yulin shekarar 2014 bisa shiga tsakanin kasashen duniya wanda Aljeriya ta jagoranta.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China