in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta nuna rashin jin dadi game da jinkirin da aka samu na yarjejeniyar zaman lafiyar Mali
2018-01-25 11:05:01 cri

Mambobin kwamitin sulhun MDD sun bayyana rashin jin dadinsu game da abin da suka bayyana da rashin hakuri gami da jan kafa wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar kasar Mali.

Mambobin kwamitin tsaron MDD sun yiwa manema labarai karin haske bayan ganawarsu da mataimakin sakatare janar mai kula da al'amurran zaman lafiya na MDDr, Jean-Pierre Lacroix, dangane da halin da ake ciki a Mali.

Sanarwar da kwamitin tsaron MDDr ya fitar ta nuna bukatar dake akwai ta daukar kwararan matakai da za su kawo zaman lafiya ga al'ummar arewaci da sauran sassan kasar ta Mali domin cimma nasarar mutunta yarjejeniyar zaman lafiyar mai dorewa, don gudun yiwuwar sake mayar da hannun agogo baya game da sha'anin zaman lafiya da tsaron kasar.

Sanarwar ta sake jaddada muhimmancin samun ingantaccen ci gaba kafin aiwatar da zaben kasar ta Mali dake tafe a cikin wannan shekara ta 2018. An bukaci dukkan bangarorin kasar da su dauki alhakin tabbatar da ganin an aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China