in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi kira ga manyan kasashen duniya su girmama ikon mallakar kasar Syria
2018-04-16 11:03:55 cri

Tarayyar Afrika AU, ta yi kira ga manyan kasashen duniya su hada hannu wajen warware yakin basasar kasar Syria tare da girmama 'yancin mallakar kasar.

Wata sanarwa da shugaban hukumar AU Moussa Faki Mahamat ya fitar, ta yi tir da amfani da makamai masu guba, sannan ta bukaci a ba da muhimmanci ga hadin kan kasashen duniya wajen samar da mafita mai dorewa a siyasance, ga yakin basasar kasar saboda makomar al'ummar kasar kadai.

Sanarwar ta ce, nahiyar Afrika na sa ran mambobin kwamitin sulhu na MDD, musammam na din din din, za su ajiye banbancin dake tsakaninsu tare da yin dukkan mai yiwuwa wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya domin amfanin dukkanin bil'adama, wanda ya dace da nauyin da dokokin MDD suka dora musu.

Har ila yau, AU ta ce tana goyon bayan hadin kan kasa da kasa, kuma dole ne duk wani matakin da za a dauka, ya kasance bisa dogaro da kwararan shaidu da hukuma mai zaman kanta da nagarta da adalci za ta gabatar, tare da kiyaye dokokin kasa da kasa, ciki har da ikon da kwamitin sulhun ke da shi na neman taimako. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China