A jawabinsa, Guterres ya ce, a shekaru 11 da suka wuce, a wajen babban taron MDD, an yanke shawarar kebe wannan rana, wato ranar duniya kan tunawa da mutanen da tsarin cinikin bayi, gami da cinikayyar bayin ta tekun Atlantika ya ritsa da su. Makasudin yin hakan shi ne, baya ga baiwa jama'a damar sanin wannan tarihi, akwai kuma kara fadakar da kasashen duniya kan hadarin dake tattare da kabilanci, da nuna wariyar launin fata.
Antonio Guterres ya kuma yi kira ga kasa da kasa, da su ci gaba da yaki da ayyukan da suka shafi yin lalata, gami da cin zarafin jama'a, da tabbatar da cewa, kowane mutum zai iya rayuwa da sana'arsa cikin adalci da mutuntawa. (Murtala Zhang)