in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zaman lafiya ya dawo Abuja bayan arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga
2018-04-18 11:24:44 cri

Zaman lafiya ya dawo birnin Abuja, fadar mulkin Nijeriya a jiya Talata, bayan arangamar da aka yi tsakanin 'yan sanda da daruruwan masu zanga-zanga a ranar Litinin.

An ga jami'an tsaro dauke da makamai a manyan titunan tsakiyar birnin a jiya Talata, ciki har da titin dake kai wa majalisar dokokin kasar da kuma sakatariyar gwamnati.

Wani tattaki da mabiya Shi'ar suka yi a ranar Litinin domin neman sakin shugabansu, ya rikide zuwa rikici bayan sun farwa wasu ayarin 'yan sandan kwantar da tarzoma.

Arangamar ta hadadda mutuwar mutum guda da aka bindige yayin da wasu da dama suka jikkata.

Rikicin dai ya janyo tsaiko ga harkoki a wasu sassan birnin na tsawon sa'o'i.

A cewar rundunar 'yan sandan kasar, jami'anta 22 ne suka jikkata yayin hatsaniyar.

Yan sanda sun zargi masu tattakin da farwa jama'ar da ba su ji ba, ba su gani ba, inda suka janyo tsaiko ga harkokin kasuwanci da tituna, tare da fasa gilasan motar mutane yayin tattakin.

Mabiya darikar Shi'a sun gudanar da zanga-zangar ne domin neman a saki shugabansu Ibrahim El-Zakzaky wanda ke hannun 'yan sandan farin kaya tun a watan Disamban shekarar 2015, bayan rikici ya barke tsakanin mabiyansa da sojoji a jihar Kaduna dake arewa maso yammacin kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China