in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta amince da gudanar da asibitoci ta intanet
2018-04-17 09:46:20 cri

Kasar Sin ta amince da gudanar da asibitoci ta intanet, sai dai ta ce dole ne su kasance masu aminci.

An bayyana haka ne yayin taron manema labarai kan manufofin gwamnati da ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar ya saba gudanarwa.

A cewar wata jami'ar hukumar lafiya ta kasar Jiao Yahui, cibiyoyin kiwon lafiya za su iya kafa asibitoci ta intanet domin gudanar da ayyuka, haka zalika su ma kamfanonin dake ba da hidimar intanet din za su iya gudanar da irin asibitocin, kuma dole ne su gudanar da ayyukansu bisa ganawa ido da ido da marasa lafiya.

Ta ce, gwamnati za ta gaggauta fitar da ka'idojin ba da hidimar kiwon lafiya ta kafar intanet, tare da bayyana abubuwan da ake bukata da hanyoyin da za a bi wajen neman izinin gudanar da asibitocin.

Ana sa ran matakin zai bunkasa harkokin kiwon lafiya ta intanet a kasar, wanda ke samun ci gaba cikin sauri.

Shafukan tuntubar likita da kamfanoni masu samar da sabbin hidimomin fasaha suka samar, ya samu karbuwa sosai a kasar cikin shekarun baya-bayan nan.

Ta shafukan website da manhajar waya, mutane za su iya zabar likita mafi kwarewa a fadin kasar don duba su. Bisa dogaro da hotunan lafiya da bayanai da za a aike ta intanet, likitoci za su iya ba da shawarwari, amma dai suna bukatar ganin marasa lafiya ido da ido, don duba su da ba su magunguna da sauran abubuwa. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China