A jiya ne kasar Rasha ta hau kujerar naki kan wani daftarin kwamitin sulhun MDD dake neman karawa kwamitin bincike mai zaman kansa da aka nada kan zargin da ake yiwa kasar Syria na amfani da makamai masu guba kan fararen hula.
Kudurin wanda kasar Amurka ta gabatar, yana neman a karawa kwamitin binciken da MDD da kungiyar haramta amfani da makamai masu guba suka kafa da wa'adin shekara daya. Sai dai kudurin ya gamu da turjiya, yayin da mambobin kwamitin 11 suka goyi bayansa, kasashen Sin da Kazakhstan kuma suka kauracewa kada kuri'ar, yayin da mambobi biyu kuma suka ki goyon bayan kudurin.
Gabanin kada kuri'ar, jakadan Rasha a MDD Vassily Nebenzia, ya nemi a dage zaman tattauna karin wa'adin kwamitin na JIM zuwa ranar 7 ga watan Nuwamban, bayan kwamitin binciken ya gabatar da rahotonsa.
Sai dai kuma jakadan kasar Burtaniya a MDD da mataimakin wakilin kasar na din-din-din a MDDr, sun bayyana matakin kasar ta Rasha a matsayin kafar ungulu, kana wani yunkuri na jan kafa.
A ranar 17 ga watan Nuwamban wannan shekarar ce wa'adin kwamitin binciken na JIM da aka kafa kan zargin da ake yiwa Syria na amfani da makamai masu guba kan fararen hula zai kare.(Ibrahim)