in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta ce nasarar gudanar da zabe a DRC na da muhimmanci ga zaman lafiya a yankin Great Lakes
2018-04-11 09:31:31 cri

MDD ta ce nasarar gudanar da zabe a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo DRC na da muhimmanci matuka ga tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Great Lakes na tsakiyar Afrika.

Yayin wata muhawara da kwamitin sulhu ya gudanar game da yanayin yankuna, wanda ya hada da batutuwan jin kai da ayyukan kungiyoyin tsageru, masu jawabi sun bayyana cewa, sahihin zabe a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da kuma nasarar mika mulki cikin ruwan sanyi zai yi gagarumin tasiri kan tabbatar da zaman lafiya da kawanciyar hankali da kuma ci gaba a yankin na Great Lakes.

Wakilin MDD na musammam a yankin Said Djinnit, ya bukaci kwamitin ya ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki daya, game da goyon bayansa ga aiwatar da yarjejeniyar siyasa da aka cimma ranar 31 ga watan Disamban shekarar 2016 tsakanin shugabannin siyasar kasar, wadda a karkashinta ne za a gudanar da zabe a ranar 23 ga watan Disamban bana, domin zabe wanda zai maye gurbin shugaban kasar Joseph Kabila.

Said Djinnit, ya ce yankin Great Lakes na cikin yankuna mafiya sarkakiya na Afrika, amma kuma yana daya daga cikin wadanda za su ba da gagarumar gudunmuwa ga zaman lafiya da ci gaban nahiyar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China