in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin kunar wake ya halaka mutane 10 a Najeriya
2018-01-18 09:32:16 cri

Rundunar 'yan sandan jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin Najeriya ta bayyana cewa, mutane 10 ne suka gamu da ajalinsu, kana wasu 65 kuma suka jikkata sakamakon wasu tagwayen hare-haren kunar wake da ake zargin mayakan Boko Haram da kaddamarwa

Kwamishinan 'yan sandan jihar Damian Chukwu wanda ya sanar da hakan, ya ce wasu mutane biyu ne da ake zargin 'yayan kungiyar Boko Haram ne da tayar da abubuwan fashewa a kasuwar Muna Garage dake wajen birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, fashewar da a cewar Damian Chukwu, ta haddasa mummunan barna.

Ya ce, fashewa na farko ya faru ne a mashigar kasuwar, yayin da na biyun kuma ya tashi a tsakiyar kasuwar.

Mai magana da yawun hukumar bayar da agajin gaggauwa ta kasa Abdulkadir Ibrahim, ya ce kimanin mutane 65 ne suka jikkata sakamakon wadannan hare-hare. Kuma yanzu haka suna karbar magani a asibiti.

A shekarar da ta gabata, yankin na Muna ya fuskanci hare-haren kunar wake da ba su gaza 12 ba, inda harin na jita Laraba ke zama irinsa na farko a wannan shekara.

Ana zargin Boko Haram da halaka rayukan mutane sama da 20,000, baya ga wasu miliyoyi da suka bar mutsugunansu tun lokacin da kungiyar ta fara kaddamar da hare-hare a shekarar 2009. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China