in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bo'ao, ya sake zama wuri mai ni'ima
2018-04-08 15:39:18 cri

Manufar Yin Gyare-gyare A Gida Da Bude Kofa Ga Kasashen Waje: Sirri Ne Wanda Kasar Sin Ba Ta Boye Ba Wajen Tabbatar Da Kara Samun Ci Gaba

A watan Disamban shekarar 1978, a yayin cikakken zama na 3 na kwamitin tsakiya na karo na 11 na JKS, an tsai da kudurin yin gyare-gyare a gida da bude kofar kasar ga kasashen waje, don haka kasar Sin da tsawon tarihinta ya kai fiye da shekaru dubu 5 ta bude kofarta ga kasashen waje don radin kanta.

A watan Oktoban shekarar 2013, a yayin cikakken zama na 3 na kwamitin tsakiya na karo na 18 na JKS, an tsai da kudurin zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje daga dukkan fannoni. Cikin kwanaki fiye da dubu 1 da suka wuce, sau 39 ne shugaba Xi ya shugabanci taron kungiyar dake jagorantar aikin zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje daga dukkan fannoni karkashin shugabancin kwamitin tsakiya na JKS, inda aka fito da matakai fiye da 1500, wadanda suka mai da hankali kan yin gyare-gyare a fannonin tattalin arziki, siyasa, al'adu, zaman al'ummar kasa, muhalli, kyautata JKS da dai sauransu, lamarin da ya samu manyan sauye-sauye da dama a tarihi.

A watan Maris na shekarar 2018, an daga matsayin kungiyar zuwa kwamitin da zai jagoranci aikin zurfafa gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje daga dukkan fannoni.

Sakamakon saurin bunkasar dinkewar tattalin arzikin duniya, da kuma takara mai zafi a tsakanin kasa da kasa ta fuskar karfin kasa, ya sa ba tare da rufa-rufa ba, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi bayani a yayin da yake zantawa da wakilin gidan telebijin na kasar Rasha inda ya ce, idan kasar Sin ta son kama zarafi, domin kara samun sabon ci gaba, sai ta dogaro da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje.

A ganin wannan shugaban koli na kasar Sin, a tarihin dan Adam, ba a taba ganin wata babbar kasa mai yawan mutane fiye da biliyan 1.3 da ta zamanintar da kanta ba. Don haka dole ne kasar Sin ta bi hanyarta wajen samun ci gaba. Dole ne ta yi ta yin gwaje-gwaje. Sa'an nan dole ne ta rika zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje domin ta samun ci gaba.

A matsayin harkar diplomasiyya ta farko da kasar Sin ta yi a gida a shekarar 2018, kassahen duniya na sa ran sauraren muryar kasar Sin a sabon zamani a garin Boao mai ni'ima. (Sanusi Chen, Tasallah Yuan)


1  2  3  4  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China