in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bo'ao, ya sake zama wuri mai ni'ima
2018-04-08 15:39:18 cri

"Ziri Daya Da Hanya Daya": Sabuwar Shawarar Kara Bude Kofar Kasar Sin Ga Ketare

A lokacin da aka yi tambaya da ba da amsa a yayin taron Bo'ao, a lokacin kaka na shekarar 2013, a yayin da ya kai ziyara kasashen tsakiyar Asiya da na Gabas maso kudancin Asiya, bi da bi, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar da shawarar bunkasa "zirin tattalin arziki mai bin hanyar siliki" da "hanyar siliki dake kan teku ta karni na 21", ta yadda kasashen dake kewayen zirin da hanyar za su iya gina su cikin hadin gwiwa. Sabo da haka, shawarar "Ziri daya da hanya daya" ta kasance tamkar wani sabon yanayi, inda kasar Sin da sauran kasashen duniya za su iya tattauna tare, da neman bunkasa, da kuma cin gajiya tare.

A lokacin da Xi Jinping ya tabo dalilin da ya sa ya gabatar da wannan shawararsa. Ya ce, "ina son dukkanin kasashen duniya su iya samun bunkasa tare a yayin da kasar Sin ke samun ci gaba."

A ganin masana, shawarar "ziri daya da hanya daya" ta kasance tamkar wani sabon dandalin da kasar Sin ta gina, inda kasashen duniya za su iya yin hadin gwiwar neman ci gaban tattalin arzikinsu tare.

Kasar Sin ta bude kofarta ga sauran kasashen duniya baki daya, ba domin gina wani lambun shan iska nata kawai ba, a'a burinta shi ne fatan gina wani lambun shan iska wanda sauran kasashen duniya ma za su iya jin dadi a cikinsa. A cikin shekaru 5 da suka shige, kasar Sin ta dauki matakai daban daban domin more ribar da ta samu a lokacin da take neman samun ci gaba, ta yadda ita da sauran kasashen duniya, za su iya samun nasara cikin hadin gwiwa.

Alal misali, kasar Sin ta kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa da kasashe fiye da 40, da wasu kungiyoyin kasa da kasa, sannan ta fara yin hada hannu da kasashe fiye da 30 a fannin bunkasa masana'antu, a yayin da ta zuba jari na fiye da dalar Amurka biliyan 50 a kasashen da suke kewayen "ziri daya da hanya daya". Bankin zuba jari kan kayayyakin more rayuwar al'umma na Asiya, ya riga ya samar da rancen kudi kimanin dalar Amurka biliyan 1.7 ga kasashen dake bin shawarar "ziri daya da hanya daya". Sannan masana'antu da kamfanoni na kasar Sin, sun gina shiyoyyin hadin gwiwa na bunkasa tattalin arziki da cinikayya 56 a kasashe fiye da 20, inda aka samar wa kasashen da abin ya shafa harajin dalar Amurka kusan biliyan 1.1, tare da guraben aikin yi dubu 180.

……

1  2  3  4  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China