in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bo'ao, ya sake zama wuri mai ni'ima
2018-04-08 15:39:18 cri
A lokacin bazara na shekarar 2018, an sake bude "lokacin Bo'ao". Lardin Hainan, wato yankin musamman mafi girma dake gwajin manufofin bunkasa tattalin arziki, da bude kofa ga ketare a nan kasar Sin, ya sake jawo hankulan sauran kasashen duniya.

Yau shekaru 5 da suka gabata, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi wa duk duniya alkawarin cewa, "kasar Sin ba za ta girgiza manufarta ta yin gyare-gyare da bude kofarta ga ketare ko kadan ba". A ran 10 ga watan Afrilu mai zuwa, zai bayyana wa duk duniya sabon shirin yin gyare-gyare, da bude kofa ga ketare na kasar Sin.

Tambaya Da Amsa Na Bo'ao: Kasar Sin Ba Za Ta Rufe Kofarta Da Ta Riga Ta Bude Wa Sauran Kasashen Duniya Ba

A shekarar 2013, wasu masu tafiyar da kamfanoni da masana'antu na gida da na waje 32, wadanda suka halarci taron shekara-shekara na Bo'ao na Asiya sun taba halartar wani taron karawa juna sani tsakaninsu da shugaba Xi Jinping.

Zein Abdalla, babban jagoran kamfanin Pepsi na kasar Amurka, ya yi fatan gwamnatin kasar Sin za ta kara bude kofarta ga ketare, kuma yana fatan gwamnatin kasar Sin za ta hanzarta yin gyare-gyare kan yadda hukumomin gwamnati za su kara saurin dudduba takardun da kamfanoni ke gabatar, sannan za ta iya fitar da manufofin sa kaimi ga baki 'yan kasuwa, da su zuba jari a fannonin aikin gona da tattalin arziki maras gurbata muhalli.

Sannan shi ma babban jagoran kamfanin Fortescue Metal Group na kasar Australiya Forrest ya ce, sakamaon kara shigo da duwatsun karfe da kasar Sin ke yi daga kasar Australiya, kamfaninsa ya zama daya daga cikin kamfanonin albarkatu wadanda suka fi samun nasara a duk duniya. Sabo da haka, zai ci gaba da zuba karin jari a kasar Sin, a yayin da yake kara bayar da gudummawarsa ga bunkasar zaman al'ummar Sin.

Babban direkta kuma jagoran kamfanin Chia Tai, wato kamfanin Charoen Pokphand na kasar Thailand Dhanin Chearavanont ya ba da shawarar cewa, ya kamata kasar Sin ta kara bukatun da ake da shi a kasuwar gida, ta yadda za a iya kawo kyakkyawan tasiri ga bunkasar aikin gona, da sana'o'in ba da hidima, sannan karin kamfanoni su iya zuba jari a fannonin da suke shafar aikin gona, da bunkasa yankunan karkara, da harkokin manoma.

……

A yayin taron, shugaba Xi Jinping ya ba da amsa cike da imanin cewa,

——Mun tabbatar da burin da za mu cimma domin "shekaru dari " guda biyu, a yayin da muka gabatar da cimma burin farfadowar al'ummar Sinawa. Tabbas za a shigar da sabon karfi domin kokarin cimma wadannan buri namu. Bisa kokarinmu, tabbas ne za a iya tabbatar da samun wani kyakkyawan saurin bunkasa tattalin arzikinmu.

——Dukkannin kamfanoni da masana'antun da aka yiwa rajista a yankin kasar Sin, sun zama muhimman bangarorin tattalin arzikin kasar Sin. Ba za mu canja manufarmu ta yin amfani da jarin waje ba, kuma dole ne za mu ci gaba da kare 'yancin halal na jarin waje bisa doka. ——Kasar Sin za ta kara bude kofa ga ketare a karin fannoni da matakai daban daban, domin daga matsayinta na bunkasa tattalin arzikinta. A waje daya, muna adawa da kowane nau'in mataki na kashin kai. Muna fatan za a iya kawar da matsalolin tattalin arziki da cinikayya dake kasancewa a tsakanin kasa da kasa kamar yadda ya kamata ta hanyar yin tattaunawa, ta yadda za a iya kafa wani tsarin samun daidaito da moriya, tare da kulawa da bunkasa tattalin arziki da cinikayya.

1  2  3  4  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China