in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bo'ao, ya sake zama wuri mai ni'ima
2018-04-08 15:39:18 cri

Yankunan Gwaje-gwaje Na Yin Ciniki Cikin 'Yanci: Yankunan Kasar Sin Na Bude Kofarta Ga Kasashen Ketare

Birnin Shanghai, wanda shi ne mafarin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, yana cikin rukuni na farko na biranen kasar Sin da ke bakin teku, wadanda suka bude kofarsu ga kasashen ketare. Ya kuma kafa yankin gwaje-gwaje na ciniki cikin 'yanci a hukumance a shekarar 2013.

Bayan shekaru 2 kuma, an kafa irin wadannan yankuna a lardunan Guangdong da Tianjin da Fujian. Sa'an nan a shekarar 2017, sauran irin wadannan yankuna 7 suka kafu a birnin Chongqing, da lardunan Liaoning da Zhejiang da Henan da Hubei da Sichuan da Shaanxi, inda aka shiga sabon zamani.

Kasar Sin ta mayar da yankunan musamman na tattalin arziki guda 4 wato Shenzhen da Xiamen da Zhuhai da Shantou matsayin rukuni na farko da ta fara yin gwaje-gwajen bude kofa ga kasashen waje. Tun bayan shekarar 2013 har zuwa yanzu, yankunan gweje-gwaje na ciniki cikin 'yanci guda 11 da gwamnatin Sin ta kafa sun zama muhimmin dandali na kasar Sin wajen kara bude kofa ga kasashen waje da yin gyare-gyare a gida da kuma shiga cikin dinkewar tattalin arzikin duniya cikin sabon tsarin yau da kullum kan tattalin arziki.

Shugaba Xi Jinping ya ce, kafa yankunan gwaje-gwaje na yin ciniki cikin 'yanci, wani muhimmin mataki ne da kwamitin tsakiya na JKS ya dauka wajen kara azama kan yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a sabon zamani.

A shekaru 5 da suka wuce, wadannan yankunan gwaje-gwaje na ciniki cikin 'yanci na rukunoni guda 3 sun sha bamban a ayyukansu, tare da yin kirkire-kirkire. Yankin gwaje-gwaje na ciniki cikin 'yanci na Shanghai ya lalubo hanyoyi fiye da 100 na kulawa da ayyuka a fannin zurfafa yin gyare-gyare a harkokin zuba jari da ciniki da harkokin kudi da tsarin kulawa da ayyuka da dai sauransu. Ana iya yayata wadannan hanyoyi a wurare daban daban na kasar, kamar tsarin kulawa da jarin waje da ke cikin takardar sunayen fannonin da gwamnati ba ta bude kofa ga kasashen waje ba, da ba da sauki kan harkokin ciniki. Yankunan gwaje-gwaje na ciniki cikin 'yanci na rukuni na 3 kamar su Liaoning da Zhejiang, wadanda aka kafa shekara guda da ta wuce, sun hada kansu a maimakon gudanar da ayyuka su kadai, inda suka gaggauta sabunta tsare-tsare, ta yadda muhallin gudanar da harkokin kasuwanci ya kyautata sosai a wadannan yankuna.

1  2  3  4  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China