in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump: Amurka za ta yanke shawara ko za ta janye sojojinta daga Sham ko a'a
2018-04-04 15:30:14 cri
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana a jiya cewa Amurka za ta yanke shawara game da janye sojojinta a yankin gabas ta tsakiya ko kuma akasin haka nan bada dadewa ba, yana mai cewa matakin soja da Amurka ta dauka cikin shekaru 10 da suka shude a yankin gabas ta tsakiya na lakume makudan kudade amma ba tare da samar da wani amfani ba.

A wannan rana kuma, Trump ya gana da shugaban Estonia Kersti Kaljulaid, da shugaban Latvia Raimonds Vējonis da shugaban Lithuania Dalia Grybauskaitė dake ziyara a kasar.

Yayin taron manema labaru na hadin gwiwa da shugabannin suka yi, Trump ya ce, burin matakin soja da Amurka ta dauka a Sham shi ne murkushe kungiyar IS, kuma a yanzu ta kusan cimma wannan buri. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China