in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya nanata aniyar tsaurara matakai kan Rasha, sai dai yana fatan kyautata dangantaka tsakaninsu
2018-04-04 10:51:56 cri
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana matsayinsa na tsaurara matakai kan Rasha, sai dai duk da hakan yana fatar kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Trump yace "mai yiwuwa ne babu wanda ya isa ya tsaurara matakai kan Rasha sama da Donald Trump," shugaban na Amurka ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da wasu shugabanin kasashen yankin Baltic su uku da suka ziyarci fadar White House a jiya Talata.

Haka zalika, Trump yace, "a zahiri, muna son mu yi aiki tare da Rasha. Yin aiki tare da Rasha abu ne mai matukar kyau, ba abune dake da wata illa ba."

Dangantaka tsakanin Washington da Moscow ta yi tsami ne, tun bayan da Amurka ta sallami jami'an jakadancin Rasha kimanin 60 kana ta rufe karamin ofishin jakadancin Rashar sakamakon nuna goyon baya ga Birtaniya da sauran kasashen yammacin duniya game da batun zargin da akewa Moscow da hannu wajen yunkurin yin amfani da siradi mai guba wajen hallaka tsohon jami'in leken asirin Rasha dake Birtaniya.

Sai dai Rashar ta mayar da martani inda itama ta sallami jami'an diplomasiyyar Amurka ta kuma rufe karamin ofishin jakadancin Amurkar dake St. Petersburg.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China