in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gobara ta kashe mutane 64 a Rasha
2018-03-27 11:10:44 cri
Majiyoyi daga ma'aikatar kula da bukatun gaggawa ta kasar Rasha sun ce, gobarar da ta tashi a wani babban rukunin kantuna dake jihar Kemerovo a yammacin shekaranjiya a kasar, ta yi sanadin mutuwar mutane 64. Rasha na nan tana kokarin binciken musabbabin tashin gobarar, haka kuma ana kokarin gudanar da bincike kan irin wadannan rukunonin kantuna a duk fadin kasar, domin rigakafi ya fi magani.

Da misalin karfe 3 da minti 10 na yammacin shekaranjiya ne gobara ta tashi a rukunin kantuna mai bene hudu na birnin Kemerovo dake jihar Kemerovo na kasar, daga wurin wasan yara dake bene na hudu, inda ta wutar ta ruru zuwa sauran wurare cikin sauri, har ma hayaki mai karfi ya game ko'ina.

Ministan kula da bukatun gaggawa na Rasha ya ce an jajirce wajen gano musabbabin tashin gobarar, yana mai cewa za'a bayyanawa jama'ar kasar da zarar an samu kwararan sakamako,

A wani labarin kuma, sanarwar da gwamnatin yankin na Kemerovo ta fitar, ta ce za a yi zaman makoki na tsawon kwanaki uku a yankin daga yau Talata, domin wadanda gobarar ta rutsa da su. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China