in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin kasar Sin ya bayyana manufar kasar a fannin kula da ruwa
2018-03-25 13:06:41 cri
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD mista Ma Zhaoxu ya yi jawabi a wajen wani taron MDD dangane da shirin kula da ruwa a cikin wasu shekaru 10 da aka kayyade, inda ya bayyana manufar kasar Sin a wannan fanni.

A cewar mista Ma Zhaoxu, a zamanin da muke ciki, matsalolin karancin ruwa, da gurbacewar ruwa, da gurbacewar muhalli mai alaka da ruwa na kara tsananta. Ya ce, hakika ruwa na taka muhimmiyar rawa ga yunkurin mutanen duniya na cimma burin samun ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030, musamman ma a fannin ayyukan kawar da talauci da yunwa, da karfafa harkar kiwon lafiya da aikin jinya.

Jami'in ya kara da cewa, kasar Sin na kokarin kirkiro sabbin dabaru, da neman samun daidaituwa, da amfanawa kowa, a kokarinta na kula da ruwa. Dabarun da kasar ta dauka sun hada da kafa ka'idoji masu tsanani a fannin kula da ruwa don tilastawa tattalin arziki ya sauya fasalinsa, da sanya jama'a su yi kokarin tsimin ruwa, da kokarin magance gurbacewar ruwa, da tsabtace ruwan koguna da na tabkuna, da kara kyautata muhalli ta yadda shara da abubuwa masu dauda ba za su shiga cikin ruwan ba, da kafa wasu birane inda ake gudanar da manufofi na tsimin ruwa, da kuma kara kyautata tsarin da ake da shi na kula da ruwa a kasar ta Sin.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China