in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: A daidaita batun shan dafi da Skripal ya yi ta hanyar shawarwari
2018-03-27 20:43:48 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Madam Hua Chunying, ta bayyana a yau Talata cewa, game da batun yadda wani tsohon mai leken asiri na kasar Rasha mai suna Sergei Skripal ya sha dafi, ya kamata a yi kokarin neman sanin ainihin abin da ya faru, sa'an nan a bar kasar Birtaniya da Rasha su yi shwarwari don daidaita lamarin.

Jami'ar ta kasar Sin ta bukaci kasashe masu ruwa da tsaki, da su bi dokokin kasa da kasa, da ka'idojin kula da dangantakar kasa da kasa, da magance daukar matakan da ka iya tsananta rikici.

A kwanakin baya, batun shan dafin da tsohon jami'in kasar Rasha Sergei Skripal da diyarsa suka yi, ya haddasa gurguncewar hulda tsakanin Rasha da wasu kasashen yammacin duniya. A jiya Litinin kuma, shugaban Donald Trump na kasar Amurka ya sa aka kori wasu jami'an diplomasiyyar kasar Rasha su 60 daga kasarsa, don nuna yadda kasar Amurka ke goyon bayan sauran mambobin kungiyar tsaro ta NATO. Zuwa yanzu a kalla wasu kasashe 22 sun sanar da korar jami'an diplomasiyyar kasar Rasha wadanda yawan su ya kai fiye da 135, lamarin da ba a taba ganin irinsa ba, tun bayan kawo karshen yakin cacar baki a shekarar 1989.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China