in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta rage yawan harajin da take karba daga kamfanonin kasar
2018-03-29 10:13:54 cri

Kasar Sin ta sanar da aniyarta ta rage adadin kudaden da take caza na kayayyakin da masana'antu ke samarwa a matsayin wani bangare na rage kudaden hajari wanda aka kiyasta adadinsa kimanin yuan biliyan 400 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 63 a cikin wannan shekarar da muke ciki.

An cimma wannan matsaya ne a lokacin zaman majalisar kolin kasar Sin wanda firaiministan kasar Li Keqiang ya jagoranta a ranar Laraba. Ana fatan wannan mataki zai kara bunkasa ingancin kayayyaki a kasar.

Ana sa ran wannan sabon tsarin biyan harajin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Mayun wannan shekara, za'a rage adadin harajin ne daga kashi 17 zuwa kashi 16 bisa 100 ga kamfanoni, kana daga kashi 11 zuwa kashi 10 bisa 100 a bangaren sufuri, gine gine, sadarwa da kuma bangaren amfanin gona.

Li ya ce, sauya tsarin haraji daya ne daga cikin muhimman matakan da kasar Sin ke dauka na aiwatar da sauye sauye a fannin kudaden harajinta.

Firaiministan na Sin ya ce, a wannan karon za'a zaftare kudaden harajin ne ga dukkan kamfanoni. Da dukkannin bangarorin kasuwanci da suka yi rajista a kasar Sin, wadanda suka hada da kamfanoni na hadaka, ko kuma kamfanoni mallakar 'yan kasashen waje, dukkaninsu za'a ba su damammaki na bai daya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China