Ministan kudi na kasar Sin Xiao Jie wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a gefen taron shekara-shekara na manyan tarukan kasar biyu wato taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar da ke gudana yanzu haka a nan birnin Beijing, ya ce kasar Sin tana shirin yiwa tsarin biyan haraji gyaran fuska, ta yadda za a rika biyan haraji kan wasu kudaden albashin ma'aikata.
Ministan Xiao ya ce kudaden da iyalai masu 'ya'ya biyun ke kashewa ga misali kudin makaranta suna daga cikin wadanda za a rage harajin da ake biya a kai.
A karshen shekarar 2015 ne masu tsara dokokin na kasar Sin suka yiwa dokar tsarin iyali gyaran fuska, matakin da ya baiwa dukkan iyalai zabin haifar 'ya'ya biyu. (Ibrahim Yaya)