Mai magana da yawun fadar shugaban Najeriyar Garba Shehu, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua hakan ta wayar tarho, yana mai cewa yanzu haka an debe 'yan makarantar da suka samu kubuta zuwa wani killataccen wuri domin kula da su.
Garba shehu ya ce yana da tabbacin an saki 'yan matan, sai dai ba shi da yakini game da takamaiman yawan su a daidai lokacin zantawar tasa da Xinhua. Ya ce ba a kai ga samun cikakkun bayanai ba tukuna.
Mazauna yankin na Dapchi sun bayyana cewa, wasu mutane da suke zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne suka dawo da 'yan matan cikin wasu manyan motoci, irin wadanda aka yi amfini da su wajen kwashe su daga makarantar tasu a ranar 19 ga watan Fabarairun da ya shude.